Ƙetare
Paul Biya ya yi alƙawarin dawo da doka a Kamaru

Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alƙawarin dawo da doka a ƙasar bayan tashin hankalin da aka samu bayan zabe.
Bayyana Mista Biya a matsayin wanda ya yi nasara a zaben Ya tunzura gudanar da zanga-zanga mai muni da nuna tirjiya, wadda ta kai ga mutuwar masu zanga-zangar da dama.
Sai dai a jawabinsa na kama aiki, shugaban ya jinjinawa jami’an tsaron kasar.
Bayan shekara 43 yana mulki, shugaban ya sake nanata aniyarsa ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi mata da matasa, tare da alkawarin kawo ƙarshen cin hanci da rashawa.
You must be logged in to post a comment Login