Labarai
PCACC ta Kano ta yi taron bikin ranar yaƙi da cin Hanci da Rashawa ta duniya

Yayin da ake gudanar da bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya a yau Talata, gwamnatin jihar Kano, ta sha alwashin ci gaba da yin yaƙi da matsalar domin shawo kanta.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin bikin na bana wanda hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta gudanar a ɗakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati.
Gwamnan,wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnati Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya bayyana cewa, nasarorin da gwamnati ta samu sun haɗa da ƙwato maƙudan kuɗi da ƙadarorin da sanya dokar ta ɓaci a fannin ilimi da sauransu.
Shi kuwa shugaban hukumar ta yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC Malam Sa’idu Yahaya, kira ya yi ga al’ummar jihar Kano musamman ma matasa da su bai wa hukumarsa haɗin kai wajen yaƙi da matsalolin cin hanci da rashawa.
Da ya ke jawabi kan irin gudunmawar da hukumar ta PCACC ta Kano ke bayarwa kwamishina na ɗaya a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa Malam Musa Auyo, ya bayyana cewa ayyukan da hukumar ke yi ne ya sanya su suka kwaikwayeta inda suna M zuwa yanzu suka samu nasarori da dama.
A nasa jawabin, babban jami’i a hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta ICPC Malam Sani Tukur, ya ƙara da cewa, sun samu nasarori da dama tun bayan kafa hukumar a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo,insa ya ce ciki har da ƙwato miliyoyin kuɗi da aka wawure da samar da ofisoshin hukumar a dukka ƙananan hukumomin faɗin Najeriya.
A yayin kammala taron, hukumar ta PCACC, ta raba kayan karatu da rubutu ga ɗaliban da suka halarta, inda suka rabauta da Jakar zuwa makaranta mai ɗauke da littattafan rubutu da Kayan rubutu har ma da kayan aikin lissafi watau Mathematical Sets.
You must be logged in to post a comment Login