Labarai
PDP ta umarci mambobinta su ci gaba da shirin yin babban taronta na kasa

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta umarci mambobinta su ci gaba da shirin gudanar da babban taronta na kasa duk da umarnin wata kotu da ya dakatar da ita daga yin hakan.
Wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar Debo Ologunagba ya fitar, ta bayyana cewa, jam’iyyar PDP ta kadu da hukuncin kotun, amma ba zai kawo mata tsaiko ba.
Haka kuma sanarar ta ƙara da cewa, wani hukuncin Kotun koli na baya-bayan nan ya tabbatar da ikon jam’iyya wajen tafiyar da al’amuranta na cikin gida da kanta.
A ranar Juma’a ne wata kotun tarayya karkashin Mai Shari’a James Omotosho ta umarci jam’iyyar ta dakatar da shirin taron da ta tsara gudanarwar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba.
You must be logged in to post a comment Login