Connect with us

Labarai

PDP taki amincewa da adadin da aka keɓe mata cikin shirin ɗaukar aiki 774

Published

on

‘Yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP sun ki amincewa da karɓar adadin da aka ware musu na shirin gwamnatin tarayya wanda za’a ɗauki matasa  dubu 774 aiki a kasar nan.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Ndudi Elumelu daga jihar Delta ne ya bayyana haka yana mai cewa jam’iyyar PDP na neman da a sanya gaskiya cikin ɗaukar masu ayyukan.

Ndudi Elumelu ya ce kamata ya yi gwamnatin tarraya ta sake yin nazari kan matakan ɗaukar aikin da ta keɓewa jam’iyyar ta PDP.

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya ƙirƙiro da shirin don samawa matasa ayyukan yi a kasar nan wanda za’a dauka a kananan hukumomin 774 na kasar nan wanda za a fara daga watan Okotoban wannan shekarar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!