Labarai
PENGASSAN ta shiga yajin aiki a fadin Najeriya kan korar ma’aikata sama da 800 a matatar Dangote

Kungiyar ma’aikatan manyan jami’an man fetur da iskar gas ta Najeriya, wato PENGASSAN, ta ayyana yajin aiki a fadin kasar, tana zargin matatar man Dangote da korar sama da ma’aikata 800 bisa shiga kungiyar kwadago.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron gaggawa na majalisar koli ta kungiyar ranar Asabar, 27 ga Satumba, 2025, wacce Sakatare Janar, Lumumba Okugbawa, ya sanya wa hannu.
Kungiyar ta umurci mambobinta su daina aiki daga karfe 6 na safe ranar Lahadi, 28 ga Satumba, inda za a fara da addu’o’i na tsawon awa 24. Daga ranar Litinin, 29 ga Satumba, za a fara cikakken yajin aiki a dukkan kamfanonin mai da iskar gas, hukumomi da cibiyoyi a Najeriya.
PENGASSAN ta ce babu wani aiki da za a yi a wuraren aiki sai na kare lafiyar ma’aikata ko dukiya, wanda kuma sai da izinin babban ofishin kungiyar.
Kungiyar ta kara da cewa matatar ta maye gurbin ma’aikatan da aka kora da ‘yan Indiya fiye da 2,000, lamarin da ta bayyana a matsayin cin fuska ga ‘yan Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login