Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

‘Yan sanda sun cafke ‘yan fashi a Jigawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar damke wasu gungun ‘yan fashi, dake bin mutane har gida da makamai suna kwace musu kudi da kuma dukiya.

Rundunar ta ce, ta samu kira daga kauyen Yargaba dake yankin karamar hukumar Dutse ranar 15 ga watan Yulin da muke ciki, inda aka sanar dasu cewa, wasu ‘yan fashi dauke da muggan makamai sun shiga kauyen cikin dare, suna kwacewa mutane kayan da suka mallaka.

Sai dai da zuwan ‘yan sanda, sai suka tarar ‘yan fashin sun tsere, sai dai binciken ‘yan sanda ya samu nasarar kamo matasa 7, ‘yan kungiya daya, wadanda bincike ya nuna, su ne ke addabar mutane a Dutse da sauran sassa, wajen aikata fashi da makami.

Daya daga cikin wadanda ake zargi Isah Ali Dawa Soja wanda ya amsa cewa shine jagoransu, an same shi da kakin sojoji, da kuma bindiga kirar fiston a gidan sa, ya yin da jami’an ‘yan sandan ke gudanar da bincike.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP. Abdu Jinjiri ya shaidawa wakilin Freedom Radio Aminu Umar Shuwajo cewa, su na ci gaba da bincike, don gano sauran wadan suka gudu, da kuma irin makaman da suke amfani dashi a kauyuka suna aikata fashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!