Connect with us

ilimi

Prime College ta yi watsi da umarnin Hukumar PVIB na rufe makarantar

Published

on

Makarantar Prime College Kano, ta bayyana ƙin amincewarta da umarnin Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa-kai ta jihar Kano PVIB na rufe dakatar da ayyukanta da kuma rufe makarantar sakamakon taƙaddama kan karin kuɗin makaranta, tare da sanar da cewa ta garzaya kotu domin kare kanta.

A cikin wata sanarwa da lauyan makarantar Aliant Qais Conrad Laureate, suka fitar a yau Juma’a, makarantar ta ce, ta yanke shawarar yin magana ne bayan an mika mata umarnin kotun majistare ta Kano da ya hana ta aiwatar da karin kuɗin makaranta na shekarar 2025/2026 tare da dakatar da ayyukanta.

A watan Yulin bana ne makarantar ta sanar da ƙarin kuɗin makaranta saboda hauhawar farashin kaya da kuma bukatar ci gaba da kula da ingancin koyarwa da gine-gine.

Hukumar makarantar ta bayyana cewa, ta samar da hanyoyin sassaucin biyan kuɗi, tare da tabbatar da cewa babu ɗalibi da za a hana karatu saboda rashin biyan kuɗin makaranta.

Rahoton ya nuna cewa kashi 94 na iyaye sun biya sabbin kuɗin, amma ƙasa da iyaye 20 ne suka nuna ƙin amincewa da karin, inda suka kira makarantar da sunan “mai cin moriyar jama’a” tare da kai ƙara ga hukumar ta PVIB.

Bayanin ya ƙara da cewa sakataren gudanarwa na hukumar ta PVIB, Malam Baba Abubakar Umar, ya kai ziyara makarantar tare da wasu iyaye, sannan ya kafa kwamitin iyaye da malamai PTA na wucin gadi mai wakilan iyaye 8 da malamai 5.

Wannan kwamiti ya kada kuri’ar amincewa da karin kuɗin, amma daga baya hukumar ta PVIB, ta bayyana cewa tattaunawar ba ta kammalu ba, sannan ta bayar da umarni a janye ƙarin kuɗin.

Shugabancin makarantar ya ce, duk ƙoƙarin da ta yi don tattaunawa da hukumar PVIB ya gamu da tasgaro sai ma “zagi, raini da kuma tozarci a bainar jama’a.”

A ranar Laraba, 17 ga Satumba, makarantar ta samu umarnin kotu da ya dakatar da aiwatar da karin kuɗin da kuma dakatar da ayyukan makarantar.

Washegari, 18 ga Satumba, Radio Kano FM 98.3 ta ruwaito cewa an rufe makarantar gaba ɗaya, abin da makarantar ta ce “fassarar boge aka yi wa takardar kotun, wadda ba ta da tushe a cikin umarnin.”

A cikin sanarwar, makarantar ta ce, ta ɗauki matakin shari’a don neman adalci, tare da jaddada cewa ba za ta keta doka ba, amma kuma “rufe makaranta da dakatar da harkokin ilimin ɗalibai ba dai-dai ba ne.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!