Labaran Kano
Rabon da mu samu tallafi tun zamanin Malam Ibrahim Shekarau –Masu bukata ta musamman
Shugaban kungiyar masu bukata ta musamman ta kasa reshen jihar Kano Injiniya Musa Muhammad Shaga yace rabon da a taimaki kungiyar su wajen gudanar da ayyukanta tun zamanin gwamnatin tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau.
Injiniya Musa Muhammad Shaga ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da kungiyar yaki da yunwa ta Action Against Hunger da suka kai masa ziyara ofishin sa.
Injiniya Shaga yace duk lokacin da bikin ranar masu bukata ta musamman ta Duniya wacce ake yi duk ranar uku ga watan Disambar kowacce Shekara ta taso, zamanin gwamnatin Malam Ibrahim shekarau shi ne yake daukar nauyin komai da komai wajen tafiyar da bukukuwan.
Injiniya shaga ya shaidawa kungiyar ta Action Against Hunger cewa tun sanda Malam Ibrahim Shekarau ya sauka daga karagar mulkin jihar Kano labari ya sauya, inda yace sai dai su yiwa kansu komai tare kuma da taimakon wasu kungiyoyi.
Yace a halin da ake ciki a yanzu wasu kungiyoyi ne kadai su ke tallafa musu idan ranar ta masu bukata ta musamman ta karato.
A nata bangaren kungiyar ta Action Againts Hunger ta hannun Mrs. Gladys Ahuwan tayi alkawarin tallafawa kungiyar ta masu bukata ta musamman domin ganin an gudanar da bikin na masu bukata ta musamman da ake shirin gudanarwa ranar 3 ga watan Disambar bana.
Rubutu masu alaka:
Kungiyar dalibai ta Najeriya ta bukaci a rika gina makarantun masu bukata ta musamman