Labarai
Radiyo ta fi ko wace kafa saukin isar da sako -Dakta Adhama
Wani malami a sashen koyar da aikin jarida a jami’ar Bayero da ke Kano Dakta Ibrahim Suraj Adhama, ya bayyana Radiyo a matsayin wata kafa mai matukar muhimmanci wajen sadarwa sakamakon irin rawar da take takawa wajen wayar da kan al’umma da kuma kawo ci gaba.
Malamin ya bayyana haka ne a wani bangare na bikin ranar Radiyo ta duniya wadda take gudana a yau.
Ya ce, sakonni da da ake turawa ta Radiyo suna saurin isa sassa daban-daban cikin kan-kanin lokaci.
Malamin ya kara da cewa, duk da irin wannan zamani da ake ciki wanda kafafen sadarwa na zamani suka yi yawa har yanzu Radiyo tana kan gaba wajen samar da ci gaban al’umma ta hanyar shirye-shiryen da ake gabatarwa musamman bangaren fadakarwa, ilimantarwa tare da nishadantarwa.