ilimi
Rahoto: Inganta dakunan karatu zai kyautata harkokin ilimi a Najeriya – Sanusi
Kungiyar masana kimiyyar kula da dakunan karatu ta kasa wato Nigerian library association ta ce za ta inganta fannin domin kyautata harkokin ilimi a Najeriya.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Alhaji Sanusi Abdullahi Nasarawa ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Freedom Radio game da shirye-shiryen kungiyar kan taronta na shekara-shekara.
Alhaji Sanusi Abdullahi Nassarawa ya ce rashin isasshen kudaden gudanarwa ya durkusar da dakunan karatun a kasar nan.
Ya kara da cewa tallafin da jami’o’i ke samu daga hukumar tallafawa manyan makarantun kasar nan TETFUND ne babban dalilin da ya sa dakunan karatun ke samun damar ci gaba da kasancewa.
Sannan ya kuma ce idan har ana son gyara harkokin ilimin kasar nan wajibi ne iyaye da malamai su sanya wa dalibai akidar son karance-karance a ko wane lokaci, ba wai sai lokacin jarrabawa ba.
Alhaji Sanusi Abdullahi Nasarawa ya kuma bayyana cewa wayar hannu na taka rawa wajen hana dalibai karatu a lokacin da ya kamata.
Taken bikin na bana shi ne masana dakunan karatu su nemo duk wani mai ruwa da tsaki kan sanin muhimmancin kula da dakunan a duniya.
You must be logged in to post a comment Login