Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Rahoto : Dalilan da suka sanya ba’a warkewa daga zazzabin cizon sauro

Published

on

Masana a fannin kiwon lafiya sun alakanta yawaitar samun zazzabin cizon sauro da yanayin damuna, wanda a ko wace shekara a kan samu yawaitar jama’a da ke fama da zazzabin.

Da dama daga cikin mutane na kukan cewa su kan yi zazzabin ne sau biyu ko fiye da hakan ma, duk da matakan kariya da suke dauka.

Abubuwan da suke haddasa cutar zazzabin cizon sauro : Masana kiwon lafiya dai sun alakanta rashin tsaftar muhalli a a matsayin daya daga cikin dalilin da ke kawo taruwar sauro musamman ma barin ruwa a kwance da kuma rashin gyara magudanan ruwa.

Sai dai ko da ake alakanta yawan zazzabin da lokacin damuna, za a iya cewa har bayan damuna a kan samu masu yin zazzabin sosai, la’akari da yadda asibitoci da kuma cibiyoyin lafiya ke cika da marasa lafiya.

Sai dai jami’an lafiya na bayyana damuuwarsu kan yadda a yanzu marasa lafiya ke koma musu sau biyu ko fiye da haka, duk a sanadiyyar zazzabin cizon sauro.

To ko menene binciken masana game da rashin warkewa daga zazzabin cizon sauron da wuri, Dakta Mudassir Ahmad likita ne a sashen kula da lafiyar iyali, a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake nan Kano, ya yi mana karin haske kan wannan batu.
Ya ce “Da dama daga cikin mutane ba sa mayar da hankalin wajen shan magani a kan lokaci, da kuma shanye shi duka kamar yadda likita ya rubuta musu”.

Sai dai wasu na zargin cewa rashin ingancin maganin ke janyo rashin warkewar mara lafiya da wuri, to ko me masana a fannin harhada magunguna za su ce kan wannan batu, Alhaji Bala Maikudi shi ne shugaban kungiyar masu harhada magunguna ta kasa reshen Jihar Kano ya bayyana cewa,  “Ana  samun damowar marasa lafiya sakamakon basa shanye magun gunan baki daya”.

Yana mai cewa, “Wasu mutane suna kawo gurbatattun magunguna sannan kuma yace ajiye Magani a waje mai zafi yana sanya ya lalace”
Ya kara da cewa ajiye magunguna a dakin ajiya tsawon lokaci da kuma shan magani ba bisa ka’ida ba na taka rawa wajen kin warkewar mara lafiya, inda ya bukaci jama’a da su rinka kula da irin shagunan da za su sayi magani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!