Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rahoto: Yadda ake samar da Ƙanƙara a Kasuwar Sharaɗa da ke Kano

Published

on

Ƙanƙara ɗaya ce daga cikin abubuwan da ake buƙata a wannan lokaci na azumin watan Ramadan don sanyaya maƙoshi a lokacin buɗa baki musamman ma yadda azumin ya kasance a yanayin zafi.

Wannan ne ya sanya al’umma ke buƙatar sayen ta don sanyaya abin da za su sha yayin buɗa bakin, duk kuwa da tsadar ta.

Wakiliyar mu Zulaihat Yusuf Aji ta gudanar da zagayen gani da ido a kasuwar Sharada wanda ɗaya ne daga cikin wuraren da ake samar Ƙanƙarar a nan Kano.

Rahoton da ta tattaro ya bayyana cewa, “Kasuwar Sharaɗa cike take maƙil da jama’a ana ta hada-hadar cinikayyar ƙanƙara, a gefe guda kuma ana ɗaurawa ƙunshi-ƙunshi domin sanya ta a na’urar da zata daskarar da ita”.

Sai dai Wakiliyar ta mu ta lura da yadda matasan da ake aikin ɗura ruwan a leda ke tsumbula hannunsu a ciki ciki.

Da ma dai tuni al’umma ke zargin rashin ingancin hanyoyin samar da irin waɗannan Ƙanƙara musamman rashin tsaftar ruwan da ake ɗaurawa da kayan aikin sa baya ga rashin tsaftar masu aikin.

Abdullahi Ibrahim ɗaya ne daga cikin masu ɗaura Ƙanƙarar a Kasuwar ta Sharaɗa yace, “farashin Ƙanƙara guda ɗaya na farawa daga naira 70 zuwa 80, a sarin farashi kuma muna da rijiyar burtsatsai da muke samun ruwan ɗaurawa, sannan mun ɗauki matakin sanya hannun mu a ruwan ne don mu riƙa yin sauri, domin kuwa idan muka sanya abin diba ba zai bari muyi sauri ba”.

“Kuma a kullum muna sayar da Ƙankyara sama da ɗari da hamsin a kowanne na’ura da muke da ita, duk da cewa sai ruwan yayi a ƙalla kwana uku kafin ya zama ƙanƙara”.

Shi kuwa Shamsu Yusuf Abdullahi, bayyana irin ƙalubalen da suke fuskanta yayi musamman a ɓangaren samun wuta, inda ya ce, “Rashin wuta ita ce babbar matsalar da suke fuskanta, da kuma yadda ake buƙatar mu biya kuɗaɗen wutar ba tare da mun sha wutar da ta kamata ba, kuma dukkanin na’urorin da muke Ƙanƙarar da su suna shan wuta, domin a ciki akwai mai shan wutar dubu 3 a kullum”.

Abba Dankullo ya ce, “Dama ai ba ayi Ƙanƙarar don a sha ta ba, an yi ta ne don a dora a lemo idan yayi sanyi a sha, musamman ga masu sayar da lemon ko kuma masu bukatar abin shan su yayi sanyi, shi yasa muke ɗaura ta duk yadda ta kama, amma duk da haka muna kulawa da tsaftar ta”

Muhammadu Sadi Ɗahiru shi ne yayi magana a madadin shugabancin kasuwar masu ƙanƙarar, ya ce, “Muna sane da yadda matasan ke yin aikin samar da Ƙanƙarar, wanda hakan ne ma ya sa muka sanya dokar amfani da sanadarin tsafatace hannu da kuma tabbatar da duk mai yin sana’ar sai ya tsaftace jikin sa da kayan aikin sa”.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da buƙatar Ƙanƙarar ke ƙara yawaita sakamakon rashin wutar da ake fama da shi, wanda hakan ke haifar da tashin farashin ta a kowanne lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!