Rahotonni
Rahoto : Yau ake bikin ranar kula da marasa lafiya ta duniya
Daga Aisha Sani Bala
Wani ma,aikacin jinya a asibitin koyarwa na Aminu Kano Gambo Isa Muhammad,ya bayyana irin yarda suke kula wa da Marasa lafiya dama irin kalubalen da suke fuskanta a asibitoci.
Ya bayyana hakan ne a yau Alhamis bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta kebe don tunawa da ranar bikin baiwa marasa lafiya kulawa ta duniya.
An dai fara bikin ranar ne a babban taron da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar a watan mayun shekarar 2019 karo na saba’in da biyu a shalkwatar majalisar dinkin duniya.
A ya yin bikin ranar ta bana ,an bayyana irin manyan matsalolin da aka samu a annobar Covid19,a inda aka ambato manyan kalubalen da harkokin lafiya a duniya baki daya ke fuskata.
Masana da kuma kwararru da dama sun bayyana cewar ya zama wajibi a dinga kula da harkokin kiwon lafiya kasancewar yana bukatar ma’aikatan lafiya kwararru dan baiwa marasa lafiya kulawar data dace don samun lafiya cikin sauki, to ko marasa lafiya suna samin kulawar data Dace?
Freedom radio ta tambayi wani Mara lafiya a asibitin koyarwa na Aminu Kano kan irin kulawar da ya samu ko akasin haka yayin da bashi da lafiya?
“A gaskiya muna fuskantar matsala sosai in daka kawo marasa lafiya hajaran-majaran”
Wani ma’aikacin jinya Gambo Isa Muhammad a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya bayyana mana yadda da suke kulawa da marasa lafiya a lokacin da a kai su asibitoci.
“Ya ce duk sanda masu jinyar marasa lafiya suka kai mara lafiya suna tashin tsaye don duba shi don samun sauki”
Taken bikin ranar ta bana shine, baiwa marasa lafiya cikakkiyar kulawa domin ceto rayuwarsu.
You must be logged in to post a comment Login