Labarai
Ramat: muna sauya fasalin yadda ake rarraba wutar fitilun Titunan Kano
Hukumar kula da birni da kewaye ta jihar Kano ta ce rashin hasken fitilon a wasu daga cikin mayan titunan jihar nan, kasancewar hukumar na sake sauye-sauye don inga hasken da fitilon ke bayar wa, da kuma rage kudin da ake kashewa a duk wata wajen siyan man Gas.
Babban daraktan hukumar Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya bayyana hakan ta cikin shirin muleka mu gano na mussaman da ya maida hankali kan karancin hasken fitilo a manyan titunan jihar Kano.
Injiniya Abudullahi Garba ya ce a halin yanzu hukumar na sauya kwayayen da suka kare da wadanda suka kone da kuma wadanda suek jan wuta, kuma za’a a kammala aikin ne kafin nan da ranar Laraba mai zuwa.
Babban darakatan ya kara da cewar ya zama wajibi su sauya kwayayen da suke jan wuta daga mai cin dari hudu zuwa 60 don yin tattali, wanda haka ke nufin kowanne turki zai ci kwai mai karfin watts dari takwas yayin da zai ci watts dari 120
Freedom Radio ta rawaito cewar an dorawa hukumar dake kula da birni da kewayen jihar Kano alhakin samar da wutar lantarki da zai haskaka titunan manyan Titunan a cikin kwaryar birnin Kano da kuma kawata birnin.
Akan haka a cewar Ramat hukumar zata sami rarrar Naira miliyan dari da hamsi a duk wata, bayan da ake kasha Naira miliyan dari biyu wajen zuba man Gas a Injin Janaraito dari da Arba’in da tara da suke samar da fitilon kan tituna