Connect with us

Kiwon Lafiya

Ranar HIV: Akwai raguwar yaɗuwar cutar a Kano – Dakta Aminu Tsanyawa

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce akwai raguwar kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki da kashi 2.5 zuwa 0.5 a jihar Kano

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a bikin ranar tunawa da masu ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Ya ƙara da cewa a yanzu akwai buƙatar mutane su san matsayin su kan cutar ta HIV.

Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ƙara da cewa akwai mutane sama da dubu talatin da biyar ne suke karɓar magani a shiyoyin da aka tanadar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa yayi kira ga al’umma da su daina kyamatar masu ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!