Labarai
Ranar Ruwa: Mun samar da Rijiyoyin burtsatse 450- WIDI JALO
Gidauniyar tallafawa mabukata da marayu ta WIDI JALO ta ce, duba da matsalar rashin ruwa da wasu daga cikin Unguwanni Kano da Jihohin kasar nan ke fuskanta za ta ci gaba da samar da Rijiyoyi da Kuma fanfunan burtsatse dan saukakawa al’umma.
Daya daga cikin wakilin Gidauniyar Hajiya Bilkisu Hamisu Mai Iyali ce ta bayyana hakan a lokacin da ta ke bude fanfunan ruwa na tuka-tuka da Gidauniyar ta samar a unguwar giginyu dake karamar hukumar Nassarawa a nan Kano.
Gidauniyar ta Kaddamar da bude ayyukan ne a yau Juma’a 22 ga watan Maris din shekarar 2024 a wani bangare na bikin ranar ruwa ta Duniya da ake gudanarwa a yau.
Hajiya Bilkisu Hamisu Mai Iyali ta Kuma ce zuwa yanzu Gidauniyar ta samar da Fanfunan tuka-tuka sama da Dari hudu a nan Kano da Jihohin kasar nan Harma da Jamhuriyar Nijar.
Wasu daga cikin mutanan yankin na Giginyu sun bayyana jin dadin su, sakamakon aikin samar musu da Fanfunan tuka-tukan da Gidauniyar ta WIDI JALO ta yi.
Hakan na zuwa ne a wani bangare na bikin ranar Ruwa ta Duniya da ake gudanarwa a yau 22/3/2024 wato World Water Day, inda Gidauniyar ta WIDI JALO ke bikin ranar da kaddamar da ayyukan samar da ruwa a Unguwannin birni da kauyukan Kano.
You must be logged in to post a comment Login