Labaran Wasanni
Raphael Varane zai kwashe makonni yana jinyar rauni

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce dan wasan bayan ta Raphael Varane, zai yi jiryar rauni na wasu makonni.
Varane ya samu raunin ne a wasan karshe na UEFA Nations League da kasar sa ta France ta doke Spain da ci 2-1.
Kungiyar ta Manchester ta ce Varane ya samu raunin ne a kafadar sa yayin wasan, wanda hakan yasa ya fice daga wasan kafin a tashi.
Varane dai bazai buga wasan da kungiyar sa ta Manchester za ta yi ba da Leicester City a ranar Asabar 16 ga Oktobar da muke ciki.
Kazalika dan wasan a kwai yuwuwar ba zai buga wasan gasar zakarun turai ta Champions League ba da Atalanta da kuma wasan Liverpool dana Tottenham.
You must be logged in to post a comment Login