Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wilfred Ndidi zai kwashe watanni uku yana jinya

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles kuma dan wasan tsakiya na kungiyar Leicester City dake kasar Ingila, Wilfred Ndidi, zai kwashe watanni uku ba tare da ya bugawa kungiyar sa ta Leicester City wasa ba.

Mai horar da kungiyar ta Leicester City, Brendan Rodgers, ne ya bayyana hakan inda ya ce dan wasan Ndidi, ya samu rauni ne wanda hakan ya sanya zai kwashe watanni uku ba tare da yiwa kungiyar wasaba.

A ranar Lahadin da ta gabata dan wasan Wilfred Ndidi, ya samu rauni a wasan da kungiyar sa ta Leicester City ta doke Burnley da ci 4-2, wanda hakan yasa dan wasan bai buga wasan da kungiyarsa tai rashin nasara a hannun Arsenal da ci 2-0.

Rogers ya kumace a yanzu haka kungiyar na dakon sakamakon da likitoci za su fitar nan da makonni 6 zuwa 12.

A ranar Lahadi mai zuwa dai kungiyar ta Leicester City za ta barje gumi da Manchester City a ci gaba da gasar Firimiyar kasar Ingila.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!