Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Takaddama : Majalisa ta kalubalanci Lai Muhammed kan ayyukan ma’aikatar sa

Published

on

Majalisar dattijai ta kalubalanci ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed game da wasu ayyuka da ma’aikatarsa ta gudanar a cikin kasafin kudin bana.

Ayyukan sun hada da: kammala aikin tashar talabijin na NTA a garin Gashua da ke jihar Yobe.

Majalisar ta aza ayar tambaya kan wannan batu ne bayan da ministan ya gurfana gaban kwamitin majalisar da ke kula da ma’aikatan don kare kunshin kasafin kudinsu na badi.

A cewar majalisar ta dattawa an kashe jimillar naira miliyan dari biyu da hamsin wajen aiwatar da aikin.

Shugaban kwamitin kula da ma’aikatar yada labarai Sanata Abdullahi Sankara ya ce ministan yana da tambayoyi da dama da ya kamata ya amsa kan aikin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!