Labarai
Rashawa : EFCC ta hukunta musu laifi fiye da 600 a Najeriya
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce a shekarar 2020 ta hannun kotu ta hukunta masu laifi dari shida da sittin da biyar daga cikin kararraki dubu daya da dari uku da biyar da ta shigar gaban kotuna.
Mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC, Mohammed Abba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren.
Muhammad Abba ya kuma ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan kararraki dubu bakwai da dari uku da Arba’in daga cikin kararraki dubu goma da dari da hamsin da biyu da aka shigar gaban hukumar.
Ya kuma ce hukumar ta kuma gano makudan kudade tare kwace wasu kadarori da dama daga mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Sanarwar ta ce shugaban rikon na EFCC ya kuma godewa ma’aikatan hukumar kan irin kokarin da su ke yi na aiki tare da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu, wanda hakan ya taimaka wajen samun nasarar da aka samu a shekarar ta 2020.
You must be logged in to post a comment Login