Labarai
Rashawa: Wani bincike ya bayyana Gwamnatin Nijar da yin badaƙalar kwangila
Jamhuriyar Nijar ta musanta wani zargi da yace gwamnatin da ta shude ta Mahammadou Issoufou ta bada kwangila ta haramtacciyar hanya.
Wani dan jarida mai binciken ƙwaƙwaf kuma shugaban kungiyar ƴanjaridu na kasashen yammacin Afirca masu binciken ƙwaƙwaf Moussa Aksar, ya bayyawa Freedom Radio cewa sun samu takardu miliyan dubu goma shabiyu sun kuma samu camfanoni da paspo din mutane daga ƙasashen Russia da Nijar, da kuma Senegal, wadanda suka yi kwangila ba bisa ƙa’ida ba tun a shekarar 2007.Sannan suka sake dawo a shekarar 2012, lokacin mulkin Mahammadou Issoufou.
Tunda fari dai, gwamnatin kasar mai ci, ta bakin Ministan ma’adanai Madame Hussaini Hadizatou Yakouba ta musanta wannan sakamakon rahoton, ta kuma ce da tun asali anzo ga gwamnati da an tabbatar da gaskiyar lamarin.
Daga ƙarshe kuma, ta shawarci masu gudanar da bincike irin wannan da su guji yaɗa labarin ƙarya.
You must be logged in to post a comment Login