Kiwon Lafiya
Rashin abinci mai gina jiki na haifar da matsala a ƙwaƙwalwar yara – Dakta Umar
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce, rashin samar da ingantaccen abinci mai gina jiki ga yara na haifar musu da naƙasa a ƙwaƙwalwar su.
Babban jami’i a sashin kula da abincin mai gina jiki ga ƙananan yara na ma’aikatar Dakta Umar Yahuza ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.
Dakta Umar Yahuza ya ce “Matukar yaro ya rasa abinci mai gina jiki daga shekara biyu na farko to kuwa zai samu matsala ta rashin girman jiki da rashin hazaƙa da kuma rashin wayo”.
“Cutar Tamowa da aka fi sani da ‘Yunwa’ na haifar da yawan rashin lafiya ga yaro da kuma rashin kariya daga cututtuka sakamakon rashin samun sinadaran da jiki ke bukata” in ji Dakta Umar.
Likitan ya kuma ce, binciken da suka gudanar ya gano cewa jihar Kano na kan gaba wajen yawan yaran da ke fama da cutar Tamowa.
You must be logged in to post a comment Login