Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

RASHIN AIKIN YI : Mutane sama da miliyan biyar ne suka cike N-power

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce sama da mutane miliyan biyar ne suka yi rajistar shiga cikin shirin samar da aikin yin a wucin gadi na gwamnatin tarayya wato NPOWER.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ministar kula da harkokin jinkai takaita abkuwar ibtila’i da ci gaban jama’a, Halima Oyelade.

Sanarwar ta ce rajistar da aka fara a ranar 26 ga watan shekaran jiya na Yuni an tsara ne tun farko za a kammala a ranar 26 ga watan jiya na Yuli amma sakamakon mabukata shiyasa aka kara wa’adin da mako biyu.

Haka zalika sanarwar ta kara da cewa ya zuwa shekaran jiya lahadi tara ga wannan wata adadin wadanda suka yi rajistar shiga shirin na NPOWER sun kai miliyan biyar da dubu arba’in da biyu da daya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!