Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Athletico Madrid da Manchester United sun tashi wasa 1-1

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Athletico Madrid daga kasar Spain da Manchester United sun tashi wasa 1-1 a gasar cin kofin zakarun turai Champions League

Gumurzu tsakanin kungiyoyi biyun ya gudana a ranar Laraba 23 ga Fabrairu a filin Wanda Metropolitano da ke kasar Spain.

A minti na 6 da fara wasan matashin dan wasan kasar Portugal Jao Felix ya zura kwallon farko.

Sai dai a minti na 79 bayan dawowa zagaye na biyu dan wasa A. Elanga ya warware kwallon da aka zura musu a raga.

Wannan dai wasa zagaye na farko ne na kungiyoyi 16 a gasar, inda a ranar 15 ga Maris Manchester United zata karbi bakuncin Athletici Madrid domin sanin kungiyar da zata kai wasan kusa da na kusa da karshe a gasar.

A daya wasan da ya gudana a ranar Larabar Benfica daga kasar Portugal da Ajax daga Holland sun tashi wasa 2-2.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!