Labarai
Karya tsarin dimukraɗiyya shi ne tushen matsalar siyasa – Ɗantiye
Tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Garki da Ɓaɓura Nasir garba Ɗantiye ya ce, ƴan Najeriya sun yi hannun riga da tsarin dimukraɗiyya shiyasa har yanzu ba’a samu ci gaba a ɓangaren siyasa ba.
Ɗantiye ya kuma ce ba’a gudanar da sahihan zaɓe shiyasa ake samun baragurbin shugabanni a ƙasar.
Nasir garba Ɗantiye ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
“Na ƙalubalanci dukkanin jam’iyyu su fito su ce suna bin tsari da dokokin yadda aka tsara jam’iyyunsu da kuma dimukraɗiyya.”
“Ana samun rigingimun cikin jam’iyya ne saboda ba’a bin abinda dokar jam’iyya ta ce sai abinda iyayen gida suka ce.”
Nasir Garba ya kuma ce babu amana a tsakanin 6an siyasa shiyasa ba’a yin abinda ya dace, kazalika idan mutane suka san haƙƙinsu akan shuwagabanni to za’a samu sauyi a siyasar Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login