Labarai
Rashin fahimtar aikin mu ne yake haifar da koma baya a yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi – NDLEA
Hukumar hana sha a da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta zargi cewa rashin kyakyawar fahitar ayyukan hukumar ne ke haifar koma baya a yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Shugaban hukumar Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radio.
Abubakar Idris Ahmad wanda ya kasance sabon shugaba a hukumar bayan ya karɓi aiki a hannu Dakta Isah Likita.
Ya ce “Babban ƙalubalen da muke fuskanta a yanzu shi ne rashin kyakyawar fahimta da kuma bada gudummawa yadda ya kamata daga ɓangaren al’umma wanda hakan ke zama tarnaƙi a ayyukan mu”.
Sai dai ya zargi ƙaruwar ayyukan shaye-shaye da sakacin wasu iyaye musamman rashin sanya ido kan shige da ficen yaran su, da kuma bibiyar abinda suke aikatawa a gida da waje.
“Kuma muna samun ƙalubale daga wasu iyaye na rashin kawo yaran su hukumar mu don mu basu shawarar yadda za su hana yaran su shaye-shaye tun farkon farawarsu” in ji Abubakar Idris Ahmad.
Shugaban ya kara da cewa akwai wasu halaye da ma alamomi da iyaye za su gani a tattare da yaran su idan sun fara ta’ammali da miyagun ƙwayoyi domin su gaggauta ɗaukan mataki.
You must be logged in to post a comment Login