Labarai
Rashin kayan aiki ke ta’azzara matsalar tsaro a Najeriya – AIG Hadi Zarewa
Masanin harkokin tsaro a Najeriya kuma tsohon mataimakin sufeton ƴan sanda Muhammad Hadi Zarewa AIG mai ritaya (MNI), ya ce matsalar tsaro a Najeriya rashin kayan aiki ne da rashin wadatattun jami’ai a hukumomin tsaro.
Tsohon Sufeton ya bayyana hakan ne a yau ta cikin Shirin Barka da Hantsi daya gudana yau a nan tashar Freedom kan irin matsalolin tsaro ake fuskanta a Najeriya.
Alhaji Muhammad ya kuma ce, matsalar tabarbarewar tsaro ya kai ace gwamnati tarayyya ta rinka sanya dokar ta baci a dukkanin yankunan da suke fama da matsalar ta tsero.
Ya kuma ce, “baya goyon bayan gwamnati kan ta nemi sulhu da ‘yan-ta’ addan kasar nan”.
Ya kuma yi kira ga mahukunta da ‘yan siyasa da su kasance masu kishin kasar su koda sun sauka daga mulki ta hanyar tabbatar da daukar ingantattun kuma kwararrun jami’an tsaro da basu kulawa yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login