Barka Da Hantsi
Rashin koyarwa da harshen uwa ne ya haifar da naƙasu a ɓangaren Ilimi – Farfesa Miko Yakasai
Cibiyar ƙwararru kan aikin fassara da tafinta ta kasa tce, rashin amfani da harshen uwa wajen koyar da darussa me ya haifar da koma baya a ɓangaren ilimi.
Kazalika cibiyar ta alaƙanta yawan faɗuwar ɗalibai jarrabawa da rashin koyarwa da harshen na uwa.
Shugaban cibiyar Farfesa Hafizu Miko Yakasai ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Shirin ya mayar da hankali kan bikin ranar fassara ta duniya da za a gudanar a ranar 30 ga watan Satumba.
Farfesa Hafizu ya ce “ƙasashe da dama kan yi amfani da harsunansu wajen koyawa yaransu ilimi kuma shi yasa suke ganin ci gaban ilimin yaran su”.
Farfesan y kuma ce kamata yayi a riƙa fifita yaren Hausa sama da yaren ingilishi domin samun ci gaba a ɓangarori da dama.
You must be logged in to post a comment Login