Labarai
Rashin kwararrun malamai ya kawo koma baya a fannin ilimin kimiyya –KASSOSA
Kungiyar tsoffin daliban Kwalejojin Kimiyya na jihar Kano da Jigawa KASSOSA ta bayyana damuwarta kan rashin kwararrun malamai a fannin da kuma rashin kayan aiki.
Tsohon shugaban kungiyar daliban kuma shugaban kwamitin gudanar da zaben kungiyar ta KASSOSA Muhammad Ja’afar Na’abba ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi, na nan tashar Freedom Radio.
Muhammad Na’abba ya ce, kungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin kimiyya da fasaha a ko wane bangare, sai a yanzu akwai banbanci tsakanin ilimin kimiyya a shekarun baya da kuma yanzu.
Ya ce, rashin na’urorin aiki da kuma rashin kwararrun malamai ya taka rawa wajen tabarbarewar ilimin kimiyya a kasar nan.
Muhammad Na’abba ya yi kira ga iyaye da su rika barin ‘ya’yansu suna zabar fannin da ya kamata su karanta da kansu, domin samun nagartaccen ilimi.
You must be logged in to post a comment Login