Labarai
Rashin lauya yasa an samu tsaiko kan shari’ar AA ZAURA-EFCC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeriya EFCC, ta ce an samu tsaiko kan cigaba da shari’ar dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya Abdulsalam Abdulkarim, da akafi Sani da AA Zaura, bayan da jami’an ta suka gurfanar da shi a gaban Kotu, sakamakon rashin Lauyan sa da zai kare shi a Kotu.
A cewar hukumar ta bakin mai magana da yawun ta a nan jihar Kano Idris Muhammad, ya ce ‘wannna shi ne karo na hudu da ake samun tsaiko akan shari’ar ta dan siyasar , wanda a baya bai halarci Kotun ba a kashin kansa’.
Ya kuma ce ‘rashin halartar Kotun da lauyan AA Zauran baiyi ba a jiya Litinin, ya sa mai shari’a ya sa Muhammad Nasir Yunusa, ya daga shariar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairu mai kamawa don cigaba da gudanar da shari’ar tare da Lauyan wanda ake zargi, don bashi kariya.
Ana dai zargin AA Zaura, da Damfarar wani Balarabe dan kasar Kuwait Dalar Amurka Miliyan Daya da Dubu Dari Uku.
Rahoton: Abubakar Tijjani Rabiu
You must be logged in to post a comment Login