Labarai
Rashin manufa da aƙida ne ke sa ƴan siyasa sauya sheƙa – Farfesa Kamilu Fagge
Masanin kimiyyar siyasar nan na Jami’ar Bayero a Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce rashin manufa da aƙida ne ke sanya ƴan siyasa sauya sheƙa a dai dai lokacin da kakar zaɓe ke ci gaba da kankama.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na tashar Freedom Radio.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce “A yanzu ana siyasa ne don biyan buƙatar kai hakan ne ya sanya ƴan siyasa a yanzu ke sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa wata”.
“Babu Aƙidar dumukradiyya a zuciyar ƴan siyasa manufarsu a iya baki take da kuma buƙatar kansu, kuma shi rikicin siyasa na ragewa jam’iyya ƙarfi kuma ya na janyo ƴan jam’iyyar su yi mata ƙafar ungulu” a cewar Fagge
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya kuma ce idan har ana son kawo gyara a dumukradiyyar ƙasar nan sai wasu tsirarun mutane sun dai na ɗaukar kansu sune dumukradiyya.
You must be logged in to post a comment Login