Labarai
Rashin tabbatar wa NNPP kujerar gwamna
Jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya ta ce hana ta ko kwace mata zaben da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka.
Hakan na cikin wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami’i mai binciken kuɗi na jam’iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Kasashen Yamma ranar Laraba.
NNPP ta yi ikirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunkurin yi wa zaben mafi rinjayen al’ummar Kano zagon kasa.
Ya’yan jam’iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a Kano tun bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya sake tabbatar da soke nasarar gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf.
A ranar Laraba kuma, magoya bayan jam’iyyar sun yi zanga-zanga zuwa ofisoshin Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya da kuma Hukumar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas).
You must be logged in to post a comment Login