Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin Tsaro: Ƴan bindiga sun sace mahaifiyar wani attajiri tare da ajalin mutum guda a Kano

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun afkawa garin Rurum na ƙaramar hukumar Rano da ke nan Kano.

Rahotonni sun ce, ƴan bindigar sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 1 na daren Talata, inda suka yi awon gaba da mahaifiyar wani attajiri Alhaji Yusuf Jibrin.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Freedom Radio cewa, tun da farko maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, inda suka harbi mutane uku.

Sannan suka yi awon gaba da wani dattijo Alhaji Yusuf Jibrin wanda mahaifi ne ga attajirin da kuma uwar gidansa Hajiya Asabe Jibril.

A hanya ne kuma suka saki mahaifin nasa bayan da suka jikkata shi.

Mazaunin garin ya ƙara da cewa, ɗan uwan sa da ke cikin waɗanda harbi ya shafa Abba Yusuf Gwaɗɗu, ya rasu a asibitin Aminu Kano bayan sallar magaribar ranar Laraba.

Yayin da sauran waɗanda harbin ya shafa da magidancin da ya kuɓuta ke ci gaba da samun kulawar jami’an lafiya.

Ya ce, ba su samu ɗaukin jami’an tsaro ba a lokacin da lamarin ke faruwa har sai bayan tsawon lokaci.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawun ta, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce, mutane biyu ƴan bindigar suka yi garkuwa da su kuma tuni jami’an su, sun samu nasarar kuɓutar da ɗaya daga ciki, sun kuma shiga bincike domin ceto matar.

Wannan hari dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da sabon Kwamishinan ƴan sandan Kano ya kama aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!