Labarai
Rashin tsaro ya jefa ɗumbin mata cikin ƙangin rayuwa – Kungiyar Democratic Action Group
Ƙungiyar wanzar da zaman lafiya ta da tabbatar da dimokradiyya ta kasa wato Democratic Action Group ta ce rashin tsaro ya jefa ɗumbin mata cikin damuwa a ƙasar nan tare da jefa su cikin garari.
Shugaban Kungiyar Mustafa Muhammad Yahya ne ya bayyana hakan a yayin taron wuni guda da ƙungiyar ta shirya a wani ɓangare na ci gaba da bikin ranar Mata da aka gudanar a ranar takwas ga watan maris.
Dr Mustafa Muhammad ya ce “Mun lura cewa a yanzu mata ne ke kan gaba wajan shiga halin damuwa a ƙasar nan sakamakon yadda mazajen su suke mutuwa su barsu da ƙananan yara, wanda hakan na daga cikin dalilan da ya sanya ake ganin mata sun fi yawa a kan tituna suna barace-barace”.
“Kazalika matsalar na jefa mata cikin halin ni yasu, don haka akwai buƙatar al’umma su samar da wata hanya domin kawo sauyi kan matsalolin da ake fuskanta a yanzu, kuma hakan ne ya sanya muka shiryawa mata sama da 1000 taron yini guda domin wayar da kansu da kuma hanyoyin da za su bi idan yaransu sun shiga halin damuwa” in ji Mustapha.
Da ta ke nata jawabin a yayin taron Dr Binta Abba ta tsangayar Ilimi a Jami’ar Bayero ta Kano ta ce “Wajibi ne ga iyaye su sanya idanu kan ƴaƴansu domin kuwa a wannan lokacin akwai wasu dabi’u da yara suke aikatawa a boye ba tare da sanin iyayen su ba”.
Har ma ta ce sanya idanu kan harkokin yau da kullum na yara shi ne zai taka muhimmiyar rawa wajan kawo karshen matsalolin ra’ayin rikau ga ƙananan yara.
Ita kuwa mataimakiyar Kwamandan hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa reshen jihar Kano Hajiya Aisha Hamidu ta ce “Dole ne a riƘa sanya mata a cikin harkokin yau da kullum, domin kuwa sun fi zurfafa bincike da kuma bibiyar al’amura.
Taron wuni gudan ya samu halartar mata sama da guda dubu daya, da kuma tarin malamai da masana harkokin yau da kullum da ƴan jaridar inda kuma aka tattauna batutuwa da dama da ake ganin za su kawo mafita game da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login