Labaran Wasanni
Rashin tuntuɓar juna ya kawo tsaikon gasar NYG ta ƙasa – Mai zare
Rashin samun cikakken bayani da tuntuɓar juna tsakanin ma’aikatar matasa da wasanni ta ƙasa da hukumomin jami’ar Ilorin, ya haifar da tsaikon fara gudanar da gasar matasa ta ƙasa wato National Youth Game na 2021.
wGasar wadda aka shirya fara gufanar da ita a ranar Talata 12 ga Oktoba 2021 a filayen wasanni daban -daban na jami’ar Illorin, a babban birnin jihar Kwara.
Shugaban ƙungiyar daraktocin wasanni ta ƙasa Bashari Ahmad Maizare ne ya bayyana haka a wata zantawar sa da Freedom Radio.
Ya ce yanzu haka yanayin da ake ciki a sansanin gudanar da gasar ya munana.
“Rashin sadarwa tsakanin ma’aikatar matasa da wasanni ta ƙasa, da kuma jami’ar Illorin a wannan lokaci ya haifar da damuwa”.
“Dukkannin mu mun hallara a wajen gudanar da wannan gasar a halin da wasu ɗalibai ke yin jarrabawar su, inda muka shiga halin dimuwa”.
Ya kara da cewa ” Duk tsare-tsare an riga an kammala shi a ranar Laraba, yanzu haka za mu rankaya zuwa makarantar fasaha ta jihar Kwara, mai tazarar kilomita 7 daga jami’ar ta Illorin don samarwa da ƴan wasa da jami’an su masauki”.
Mai Zare ya ce yanayin da aka tsinci kai na rashin samun masauki a cikin Jami’ar ta Ilorin, zai shafi ƙoƙarin ƴan wasan jihohi daban-daban da tsare tsaren da suka gudanar, har ma da kashe kuɗaɗen ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum na ƴan wasa da jami’ai.
Sai dai a cewar jami’in wanda ya kasance Daraktan wasanni na hukumar wasanni ta jihar Kano, kana jagoran tawagar ƴan wasan jihar ta Kano ya ce, za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samu daidaiton lamarin, don Fara gudanar da gasar a Jumma’a 15 ga Oktoba 2021.
You must be logged in to post a comment Login