Labarai
Rashin wutar lantarki na janyowa Najeriya asarar Naira tiriliyan 11 a duk shekara– Bankin duniya
Bankin duniya ya ce rashin isash-shen wutar lantarki ya janyowa bangaren masana’antu da harkokin kasuwanci a Najeriya, asarar makudan kudade dala biliyan 29 kwatankwacin naira tiriliyan goma sha daya.
A rahoton da bankin na duniya ya fitar a jiya laraba, rahoton ya ce, harkokin kasuwanci da sana’oi a Najeriya suna tabka muguwar asarar sama da naira tiriliyan goma sha daya a duk shekara.
Bankin na duniya ya kuma yi ikirarin cewa Najeriya ce kasa da ta fi yawan adadin jama’a da ba sa samun wutar lantarki a duniya.
Babban jami’in bankin da ke kula da yammaci da tsakiyar afurka, Ashish Khanna, ya ce, rashin wutar na matukar janyo koma baya ga harkokin tattalin arzikin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login