Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: An samu tarzoma a gidan gyaran hali na Kurmawa

Published

on

Wasu fusatattun ɗaurarru sun yi ƙoƙarin arce wa daga babban gidan gyaran hali na Kano da ke Kurmawa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, inda ɗaurarrun suka yi tutsu.

Wata majiya a gidan yarin ta shaida wa Freedom Radio cewa, tarzomar ta ɓarke ne sanadiyyar zargin yi musu harambe, a yayin rabon abincin azumi da kamfanin BUA ya kai musu.

Labarai masu alaka:

Tsaro: Daurarru sun yi yunkurin tserewa daga gidan gyaran dali da ke Bauchi

Tsaro: ‘Yan bindiga sun fasa gidan gyaran hali na garin Owerri tare da sakin daurarru 1500

Amma a nata ɓangaren hukumar lura da gidajen gyaran hali ta ƙasa reshen jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta DSC Misbahu Lawan Ƙofar Nassarawa ya ce, ba haka lamarin yake ba.

Misbahu Lawan ya ce, tarzomar ta ɓarke ne a wajen waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa, bayan da jami’an hukumar suka same su da miyagun ƙwayoyi da kuma wayoyin hannu.

Wanda kuma hakan ya saɓa da dokar zama a gidan, daga bisani jami’an gidan sun kwantar da tarzomar tare da mayar da ɗaurarrun ɗakunan su.

Ya ci gaba da cewa, yanzu haka tuni aka kafa kwamitin bincike a kan lamarin, da kuma gano yadda aka shigar musu da haramtattun kayayyakin.

DSC. Misbahu Lawan ya nemi al’ummar Kano da su kwantar da hankalin su domin jami’an hukumar na iya ƙoƙarin su wajen tabbatar da zaman lafiya.

Sannan ya roƙi jama’a da su yi watsi da labarin cewa tarzomar ta ɓarke ne sanadiyyar rabon abinci.

Dangane da rahoton jin ƙara harbe-harbe a yankin gidan gyaran halin, ya ce, ba su samu wannan rahoton ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!