Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin Wutar Lantarki Ya Sanya Mata Yin Zanga-Zaga A Uguwar Sabuwar Gandu Dake Kano

Published

on

Wasu Mata mazauna yankin unguwar Sabuwar Gandu dake karamar hukumar kumbotso a nan Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana a safiyar yau Talata 21/05/2024, sakamakon rashin wutar lantarki da suke fama da ita na tsawon shekaru hudu.

Sun kuma ce tun da na’urar taransifoma dinsu ta Lalace suke fama da matsalar wutar latarkin.

Sun kuma ce sun bi duk hanyoyin da ya kamata tsawo shekarun da suka kwashe domin ganin an gyara musu wutar amma hakan su bai cimma ruwa ba.

Kazalika sun ce baya ga matsalar wutar ta latarki da suke fuskata suna fama da matsalar ruwan Sha a yankin unguwar ta Sabuwar gandu

Sun kuma ce rashin wutar latarkin na jefasu cikin mahuyacin hali musammn ma a wanan lokaci da ake fama da yanayin zafi kamar yadda mazauna yankin suka bayyana wa freedom radio

Wani dattijo malam Ibrahim Yunusa ya ce sundade suna Kai koken su ga hukumar rarraba hasken wutar latarki Kedco amma hakan su bai cimma ruwa ba.

Dan gane da haka ne mukayi kokarin jin ta bakin hukumar rarraba hasken wutar lantarki na Kano KEDCO ta wayar tarho, inda muka tuntubi mai Magana da yawunta Sai Bala sai dai be daga wayar mu ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!