Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsofaffun ‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Zaga-Zaga A Abuja

Published

on

Wasu daga cikin jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya da suka yi Ritaya sakamakon shekarun aje aikin su da ya cika, sun gudanar da zanga-zangar Lumana a birnin tarayya Abuja sakamakon watanni da suka dauka na kin biyan su kudaden Fanshon su da gwamnati ba ta yi ba.

Yan sandan sun gudanar da zanga-zangar ne a Safiyar yau Talata 21 ga watan Mayun Shekarar 2024, inda suka taru a bakin majalisar wakilan kasar nan dauke da kwalaye a hannayen su dake nuna halin da suke ciki.

Jami’an yan sandan dake da wannan matsala sun fitone daga jihohin kasar nan 27 ciki kuwa harda na birnin tarayya Abuja.

Yan fanshon dai sun bukaci gwamnatin tarayya da ta sauya musu tsarin yadda ake biyan su hakkokokin su na Fansho da hakan zai sa su rinka samun kudin su a kan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!