Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Real Madrid ta lashe gasar La Liga karo na 35

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar La Liga ta kasar Andalus a karo na 35 bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Espanyol da ci 4-0 a ranar Asabar, a filin wasa na Santiago Barnabaue.

Real Madrid dai ta lashe gasar karkashin jagorancin Carlo Ancelotti, wanda ya maye gurbin Zinedine Zidane a tawagar ta Los Blancos.

Dan wasan Real Madrid Rodrygo

Tunda fari dai dan wasa Rodrygo ne ya fara zura kwallon farko a minti na 33 da na 43 dab da za aje hutun rabin lokaci.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Real ta kara kwallo ta uku a minti na 55 ta hannun dan wasa Marco Asensio, yayinda a minti na 81 jagoran ‘yan wasan kungiyar Karim Benzema ya tabbatar da nasarar ta Madrid a wasan.

Kawo yanzu dai Real Madrid ta fi ko wacce kungiya lashe gasar, inda jumulla ta lashe har sau 35 a tarihi, sai Barcelona da ke da 26.

To sai dai Real Madrid bayan lashe gasar La Liga da ta yi zata fuskanci tawagar Manchester City a gasar cin kofin zakarun turai zagaye na biyu a mako mai zuwa a filin wasa na Santiago Bernabéu hu

Bayan da suka tashi wasan farko da ci 4 da 3 a filin wasa na Etihad da ke Ingila a makon da ya gabata.

An fara gasar La Liga a shekarar 1929 wanda kawo yanzu shekaru 93 kenan, inda Barcelona ta ka sance kungiya ta farko da ta fara lashe gasar a tarihi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!