Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

REMASAB- Taci gaba da feshin maganin sauro a kano

Published

on

Hukumar kwashe shara ta jihar kano ta ƙaddamar da feshin maganin sauro a ƙaramar hukumar Nasarawa domin samin saukin cututtuka ga al’umma musamman na zazzaɓin cizon sauro

Shugaban hukumar Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ne ya jagorancin feshin maganin sauron a unguwar Badawa dake ƙaramar hukumar Nasarawa.

Ahmadu Zago, wanda ya dami wakilcin Darakta tsare-tsare na hukumar Alhaji Yahaya Sani Abbas, ya ce sun kaddamar da aikin feshin maganin sauron a yankin Badawa, don dakile cutukan da sauro ke yadawa ga al’umma.

Ya kara da cewa za’a tabbatar an yi feshin maganin a dukkan nin lunguna da sako na unguwar Badawa, kamar yadda gwamanan jahar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kudiri aniyar hidimta wa al’umma ta bangarori da dama don samun nutsuwa da walwala a gidajen su.

Haka kuma za’a ci gaba da shiga dukkannin unguwannin da suke a faɗin jihar Kano domin ganin su anyi musu wannan feshin, don rage yaɗuwar cutuka a faɗin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!