Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abba Gida-Gida – Kuskure yadda Hizbah take kama maza da mata tana watsawa mota

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce Kuskure ne Hukumomi su rika kamo matasa maza da mata suna jefa su a cikin mota wai a matsayin gyara.

Gwamnan yayi wannan jawabin ne yayin da yake ganawa da malaman Addinin Musulunci a fadar gwamnatin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce wannan baiyi daidai da addini ba yadda wani bidiyo yake yawo a kafafen sadarwa na yadda hukuma Hizba taje wani waje a fadin kano harma da wajen da ɗalibai suke a zaune domin kama su, inda a yayin kamen akayi abin da baiyi daidai da addini ba.

Adan haka dole gwamnati tayi duba akan wannan abu da kuma samar da tsari wanda zai samarwa da al’umma musamman matasa tarbiya.

Gwamnan ya kuma ce wa’azi da addu’a shine mafita ga wanda ake ganin baya aikata dai dai ba ko aibata su ba dan haka malamai faɗakarwa ga al’umma na hannun su.

Gwamnan ya ƙara da cewa a wannan lokaci na karatowar azumin watan Ramadan gwamnatin sa tayiwa al’ummar jihar tanadin raba abinci domin rage matsin rayuwa da ake ciki.

Gwamna ya kuma tabbatar da cewa duk wasu masallatan juma’a da suke faɗin jihar nan an gyara su la’akari da yadda wasu masallatan suke babu kyan gani.

Haka kuma yace zai tabbatar da an ƙarawa dukkan nin limaman masallatan juma’a kuɗaɗen da ake biyan su kuma kuɗin zai dunga zuwa ne kai tsage daga ofishin babban akantan kuɗi na jihar domin tabbatar da daidaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!