Labarai
REMASAB ta kafa Kwamitin Kar ta-Kwana na bin dokoki da ƙa’idojin tsaftar muhalli

Hukumar Kula da Kwashen Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano REMASAB, ta kafa Kwamitin Karta-Kwana domin ƙara sa ido da tabbatar da ana bin dokoki da ƙa’idojin tsaftar muhalli a faɗin Jihar.
Kwamitin zai mayar da hankali musamman kan tsaftar kasuwanni, tashoshin mota, da sauran muhimman wurare na jama’a, tare da dakile matsalar yin bahaya a wuraren da ba su dace ba na sarari, musamman a ƙarƙashin gadar sama, da saman gada, da kuma gefen manyan tituna.
Manajan Daraktan hukumar Dr. Muhammad Salisu Khalil, ya umarci masu shagunan da ke bakin tituna da su tanadi kwandunan zuba shara domin tara shara yadda ya kamata, tare da zubar da ita a wuraren da gwamnati ta tanada.
Hukumar ta kuma jaddada cewa za ta ɗauki matakin doka mai tsauri kan duk wanda aka samu yana karya dokokin tsaftar muhalli.
Ta cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Ahmad , ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai Hukumar tare da haɗin gwiwar Kotun Tsaftar Muhalli Mobile Court, za ta ci gaba da kai samame a gidaje da wuraren kasuwanci domin hukunta duk wanda aka samu da laifin karya dokokin tsaftar muhalli.
You must be logged in to post a comment Login