Labarai
Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Wasu rahotonni sun bayyana cewa, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar shugaban Amurka Donald Trump.
A baya-bayan nan ne shugaba Donald Trump, ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaƙi maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu iƙirarin jihadi.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, inda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya wallafa a shafinsa na kafofin sadarwa cewa babu wata barazana da kiristocin ƙasar suke fuskanta.
Ana sa ran masu ruwa da tsakin a fannin tsaron za su tattauna a kan hanyoyin da za a bi wajen karfafa tsaro musamman wajen magance rikin da ke da alaka da kabilanci da suran batutuwa.
You must be logged in to post a comment Login