Labarai
Rigakafin cizon cinnaka da maganinsa idan yayi cizo
Al’umma da dama a Kano na kokawa kan wayar gari da aka yi Cinnaku sun mamayi wasu unguwanni.
Dama dai a kan fuskanci irin wannan a kowace shekara, kan hakan ne muka tattauna da masani game da cizon Cinnaka da rigakafinsa a wannan rahoto.
Yadda al’umma suka koka kan cizon cinnaka
Kafafen sada zumunta sun cika da saƙonnin jama’a game da mamayar da Cinnaku suka yi tare da gantsarawa da dama cizo.
Ga wasu da muka zaƙulo muku daga shafin Facebook.
Me ke kawo ruwan cinnaku?
Dr. Tijjani Sabi’u Imam masanin kimiyyar halittu ne a jami’ar Bayero ya yi mana bayani a kai.
Ya ce, Cinnaku suna ƙyanƙyansa a irin wannan lokaci na ƙarshen damina, inda suke yin fikafikai su yaɗu, ba wai ruwansu a ke ba.
Suna taruwa a wuraren rairayi, kuma suna da haɗin kai don haka suna zama waje guda suyi ƙwai, sannan su ƙyanƙyashe a wajen, shi ne ake ganin yawaitar Timatigayya wato Cinnaka mai fukafiki, a cewarsa.
Dr. Tijjani yace, bisa halittar cinnaka bayan sun yi ƙyanƙyasa mazansu na mutuwa su bar mata, sune kuma ke mamayar cikin gari.
Yaya cizon cinnaka yake?
Masanin ya ce, cinnaka na da wata kibiya kamar allura a wajen fikafikinsa daga nan ya ke fitar da wasu sindarai da yake tsira wa mutum mai sanya raɗaɗi.
Wane rigakafi a ke yiwa Cinnaku?
Dr. Tijjani ya ce, Cinnaku sun fi son wajen Rairayi don haka idan aka yi siminti za a rabu da su.
Na biyu a riƙa kula da ramuka a jikin katanga da malalen siminti ana toshewa.
Na uku a guji barin Duwatsu ko ina.
Na huɗu a riƙa tsaftace waje koyaushe.
Menene magani idan Cinnaka ya cije ka?
Masanin yace, da zarar Cinnaka ya gantsara maka cizo ka ɗiga ruwan Lemon Tsami nan take zai dasashe raɗaɗin.
Sannan za a iya amfani da magunan rage raɗaɗi na asibiti.
You must be logged in to post a comment Login