Labarai
Rikici ya barke tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da lauyoyinsa a kotu
Sheikh Abdulljabbar Kabara ya sake zargin lauyoyinsa a karo na biyu da rashin bashi kariya a gaban kotu.
Ya yin zaman kotun na ranar Alhamis an jiyo malamin yana cewa layoyin sun gaza kareshi sun kuma kasa bashi dama ya kare kansa.
Ana dai tuhumar Sheikh Abdulljabbar Kabara ne da laifin yin b
ɓatanci ga Annabi (SAW) lamarin da yasha musantawa.
Sai dai a ci gaba da zaman kotun na ranar Alhamis, mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya fara karɓar shaidu kan zargin da ake yiwa malamin.
Lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidu biyu, inda na farko ya ce shi ɗalibinsa ne da yake bibiyir karatunsa.
Shaidar mai suna Adamu Muhammad ya ce ya sha jin zarge-zargen da ake yiwa malamin da kunnensa.
Sai dai ana tsaka da sauraron shaidar ne Sheikh Abduljabbar ya miƙe ya ce kamata ya yi a yanke masa hukunci kisa kawai, ko kuma ya narke da dai a ce shi ne yake cin zarafin ma’aiki.
Lauyoyina ne suka hanani bayani
Malamin ya ci gaba da shaidawa kotu cewar ya nemi lauyoyinsa su bashi dama ya nunawa kotu wuraren da maganganun suka fito a cikin litattafai amma suka ƙi amince masa.
Sai dai duk da sun hana ni nunawa kotu wurnin, su kuma sun kasa kare ni a gaban kotu.
Ya ce ko kaɗan lauyoyin nasa basu kyauta masaba yadda suka hanashi kare kansa kuma suka kasa kareshi.
Malamin ya dauka a kasuwa a ke
Sai dai da yake mayar da martani lauyan Malamin Barrister Umar Muhammad ya ce Malamin ya ɗauka a kasuwa yake, yadda zai iya faɗar maganar da ya ga dama.
Ya ce tun da ya karɓi wannan shari’a yasan yana cikin hadari amma haka ya dake ya karba.
Ya kara da cewa ga mamakinsa sai gashi malamin yana kokarin zarginsa akan rashin kareshi.
Kowa ya yi hakuri
Sai dai a lokacin da malamin ya fusatane mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bai wa malamin da lauyan nasa hakuri
Haka kuma alƙalin ya umarci Abduljabbar daya daina tsoma baki a cikin shari’ar matuƙar ba buƙatar hakan akayi daga gareshi ba.
Haka kuma mai shari’ar ya sanya ranar 28 ga Oktobar da muke ciki domin ci gaba da sauraron shaida na biyu.
You must be logged in to post a comment Login