Labaran Kano
Rikicin Gwamnatin Kano da masarauta: Dattawan Arewa za su yi Sulhu
Sakamakon damuwa da dattawan arewa suka yi da rikicin da ke faruwa tsakanin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II saboda banbanci na siyasa da kuma raba masarautar Kano zuwa gida biyar kungiyar dattawan arewa sun amince su sasanta rikicin.
Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa kungiyar dattawan arewan karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ya zo ne sakamakon wani sabon rikicin da ya sake bullowa game da wa’adi da gwamnati ta bawa sarkin Kano Muhammadu Sunusi II na ya karba ko ya yaki amincewa da shugabancin majalisar sarakuna ta jihar Kano.
A sakamakon haka ne shugaban kungiyar dattawan ta arewa suka shirya tattaunawa a otel din Tahir dake birnin Kano a gobe lahadi domin tattara shahararrun mutanen arewa domin kawo karshen rikicin gwamnatin jihar Kano da masarautar.
Shugaban Kungiyar Farfesa Ango Abdullahi yace a zaman da zasu yi a Kano dattawan zasu tattauna da masu ruwa da tsaki da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da Kuma gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.