Kasuwanci
Rikicin Isra’ila da Iran ya janyo tsadar Fetur a kasashen Duniya da dama

Farashin litar man fetur a kasar nan ka iya kaiwa Naira Dubu daya kan kowace Lita, sakamakon tsadar da man yayi a Duniya da kuma tsadar canjin kudaden kasashen ketare.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar Amurka ta kaddamar da wani a hari kan ma’ajiyar makamashin Nukiliya na kasar Iran, da hakan yasa Tehran ta rufe mashigar ruwan Hormuz a wani bangare na mayar da martani.
Tuni dai dillalan mai a Najeriya suka bayyana cewa za a samu karin farashi a wasu daga cikin gidajen man a fadin Najeriya.
Ko a juma’ar da ta gabata ne kamfanin mai na Dangote ya kara farashin Fetur daga Naira 825 zuwa 880, inda kuma karin zai fi shafar yankin Arewacin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login