Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Karin farashin wuta da man fetur ya nuna Najeriya na cikin halin ni’yasu – Masani

Published

on

Masanin tattalin Arzikin na Jami’ar Bayero dake nan Kano, Farfesa Ibrahim Garba  Sheka ya ce karin farashin man fetur da wutar lantarki da gwamnati ta yi ya nuna karar tattalin arzikin kasar nan na cikin halin

Farfesa Ibrahim Garba Sheka ya ce cire tallafin da gwamnati ta yi daga fetur da kuma siyar da wutar lantarki, shi ya haddasawa hau-hawar farashin kayayyakin masarufi  da ake fama dashi a yanzu.

Don haka nan gaba ma idan gangar mai ta ci gaba da hau-hauwa a kasuwar duniya, to babu shakka farashin man fetur zai kara yin tsadar da sai mutane sunyi mamaki.

Ibrahim Garba Sheka ya kara da cewar tattalin arzikin kasar nan ya ta’allaka ne lacokan a kan fetir wanda kuma a yanzu gwamnatin tarayya ta janye tallafin da ta ke bayarwa, wanda da shi ne ake samun saukin al’amuran rayuwa.

Farfesa Garba Sheka ya kuma ce, rashin mayar da hankali wajen alkinta kayayyakin da kasar nan ke sarrafawa da kuma sauyin kudaden waje sune suka sabbaba karyewar darajar kudin kasar nan a idon duniya.

Farfesan ya jadda da cewa, bude boda shine mafita mafi sauki ga talaka zai samu sassauci ga al’amuran kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!