Connect with us

Labarai

Rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutane 11 da kone gidaje 50 a Nassarawa

Published

on

Mutane akalla 11 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da gidaje 50 suka ƙone sakamakon rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a ƙauyukan Akyawa da Udege Kasa da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Nasarawa. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga harin ramuwar gayya bayan zargin kashe wasu mutum biyu daga cikin wani bangare.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Shetima Mohammed, ya jagoranci tawaga zuwa yankin domin tantance irin barnar da aka yi tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya. Ya kuma bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasu tare da al’ummomin da abin ya shafa.

 

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta kaddamar da farautar wadanda ake zargi da hannu a harin, tare da kara tura jami’an tsaro domin dakile sake barkewar rikici. Haka kuma ana aiki tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro, yayin da aka bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu su kuma bai wa jami’an tsaro hadin kai

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!